Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Bindiga Ya Budewa Mutane Wuta a Birnin Alkahira


Wani ‘dan bindiga ya bude wuta a wajen wata Majami’a dake kudancin birnin Alkahira daura da wani kanti mallakin Krista, ya kashe akalla mutane tara ciki har da ‘dan Sanda.

Jami’ai a birnin Masar sunce an harbe maharin yayin musayar wuta da aka yi da shi jiya Juma’a a Majami’ar Mary Mina, dake a gundunar Helwan.

Wasu mutane biyar sun raunata, ciki har da ‘dan sanda, a cewar maimagana da yawun ma’aikatar lafiya Khaled Megahed.

Ma’aikatar lafiya ta Masar ta ce maharin ya mutune sakamakon harbe shi da aka yi, yayin da ma’aikatar harkokin cikin gida ke cewa maharin ya raunata kuma an kama shi da rai.

Kungiyar ISIS ta ikirarin kai harin a wata sanarwa a kafar labaranta ta Amaq.

Masu bincike sunce sun gano ‘dan bindigar, kuma yasha kai hare-hare a shekarar da ta gabata. Tun farko dai jami’an Masar sunce suna binciken yiwuwar akwai ‘dan bindiga na biyu.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG