Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Harin Ta'addanci Na Norway Ya Bayyana Gaban Kotu


Masu makoki su na ajiye furanni domin tunawa da wadanda suka mutu a harin ta'addanci na Norway

Anders Breivik ya yi imani da cewa matakan da ya dauka sun wuce gona da iri, amma kuma a ganinsa ya zama dole domin kawo juyin juya hali a kasar Norway.

A bayan da aka yi minti 35 kacal da farawa, an dage zaman sauraron hujjojin ci gaba da tsare mutumin nan da ya furta da bakinsa cewa shi ya kai harin bam tare da bindige mutane masu yawa a kasar Norway.

Masu gabatar da kararraki sun ce zasu bukaci da a tsare Anders Behring Breivik na tsawon makonni 8, amma za a iya kara wannan wa’adin kafin a fara shari’arsa.

Tun da fari, alkalin dake bin kadin wannan batun ya yanke hukumcin cewa za a yi wannan zama cikin sirri, ba za a kyale ‘yan jarida ko jama’a su shiga ba. Breivik ya nemi da a yi wannan zama a bainar jama’a domin ya bayyana wa duniya dalilansa na kai hare-haren.

Breivik yana fuskantar tuhume-tuhumen ta’addanci bisa zargin kai harin bam a ofishin firayim minista a Oslo, tare da harbe masu halartar wani taron matasa a tsibirin Utoeya dake kusa da Oslo. Jami’ai suka ce an kashe mutane casa’in da uku a hare-haren.

Lauyan Breivik yace mutumin da yake karewa ya amsa cewa shi ya kai hare-haren, amma kuma ya ce shi bai aikata wani laifi ba. Lauyan yace Breivik ya yi imani da cewa matakan da ya dauka sun wuce gona da iri, amma kuma a ganinsa ya zama dole domin kawo juyin juya hali a kasar Norway.

Kafin harin na ranar jumma’a, Breivik ya wallafa wata kasida doguwa a kan Internet, inda yake bayyana adawarsa da abinda ya kira yadda addinin Musulunci ke mamaye nahiyar Turai ta hanyar kyale Musulmi su na yin kaura zuwa can. Ya lashi takobin daukar fansa a kan ‘yan ra’ayin sassauci, yana mai zarginsu da cin amanar addinin Kirista ta hanyar yayata al’umma mai al’adu dabam-dabam.

Harin na ran jumma’a ya girgiza kasar Norway, wadda ba ta taba ganin irin wannan tashin hankali ba tun bayan mamaye kasar da sojojin Hitler suka yi a lokacin yakin duniya na biyu. Firayim minista Jens Stoltenberg yace kasar Norway ta fuskanci bala’I na kasa baki daya da wannan harin ta’addancin.

XS
SM
MD
LG