Accessibility links

Shugaba Obama Ya yi jawabi kan rikicin kasafin kudin Amurka

  • Aliyu Imam

Shugaba Obama a lokacin da yake jawabi ga Amurkawa, a daren jiya.

Shugaban Amurka Barack Obama yace idan Amurka ta kasa kara ikon karbo bashi, hakan zai yi mummunar illa da ba zai misaltu ba ga tattalin arzikin Amurka.

Shugaban Amurka Barack Obama yace idan Amurka ta kasa kara ikon karbo bashi, hakan zai yi mummunar illa da ba zai misaltu ba ga tattalin arzikin Amurka.

A daren jiya litinin ce Mr. Obama yayi jawabi ga al’umar kasar, sa’o’i bayan da shugabannin majalisun dokokin Amurka suka gabatar da shirye shirye kishiyoyi kan hanyoyin da za’a bi wajen kara ikon karbar bashi da zai hana kasar kasa biyan hakki dake kanta.

Shawarwari na makonni da suka ci tura tsakannin fadar (White-House) da majalisar dokoki , sun janyowa Amurka abinda shugaban kasar ya kira mummunar cikas. Yace idan har aka kai ga Amurka ta gaza biyan bashi dake kanta, zai kasance ganganci da rashin mutunci.

Da Yake maida martani kakakin majalisar wakilai John Boehner ya sake nanata goyon bayansa kan kwaskwarima ga tsarin mulki da zai tilastawa gwamnati aiki da abinda yake hannunta. Haka kuma ya zargi shugaba Obama da cewa baya neman hanyoyin cimma daidaito.

XS
SM
MD
LG