Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane da dan dama sun mutu sanadiyyar bam din da aka tayar a Norway


Ana iya ganin baraguzai bisa tituna bayan tashin wani bam mai karfin gaske a Oslo a yau 22 ga watan Yuli

Wani bamb mai karfin gaske ya bararraka hedikwatar gwamnatin Norway da ke Oslo, babban birnin kasar a yau Jumma’a,

Wani bamb mai karfin gaske ya bararraka hedikwatar gwamnatin Norway da ke Oslo, babban birnin kasar a yau Jumma’a, ya kashe mutane da dan dama ya kuma rautanata wasu 15.

Babbar fashewar ta kuma tayar da gobara a Ma’aikatar Man da ke kusa. Daruruwan tagogin banen mai hawa 17 sun lalace, kamar yadda ya faru da tagogin wasu gidajen masu nisan kimanin mita 400 daga wurin. Hayaki mai yawa ya yi ta fitowa daga cikin wasu ofisoshin, sannan kuma hanyoyin da ke wannan unguwar, aka santa da kwanciyar hankali, sun game da baraguzai sanadiyyar tashin bam din.

Bayan ‘yan sa’o’i, sai ‘yan sandan Oslo su ka bada rahoton cewa wani dan bindiga dadin da ya yi shigar burtu tamkar dan sanda, ya bude wuta kan wani kebabben taron matasan da jam’iyyar Labor mai mulki ta shirya. A kalla mutane biyar ne su ka sami raunuka a wannan harin. Hukumomi sun ce sun tura ‘yan sandan yaki da ta’addanci wurin kebabben taron da ke tsibirin Utoeya da ke kudu da Oslo. Ba a tantance ko akwai alaka tsakanin tashin bam din da harbe-harben ba.

A ginin hedikwatar ne ofishin Firayim Minsita Jen Stoltenberg ya ke, to amman wani mai bayani y ace das hi da ma’aikatansa duk babu wanda ya sami raunuka.

Kusan dai ba akan yi tashe-tashen hankulan siyasa ba a Norway da Oslo, inda a anan ne akan bayar da lambar yabo ta zaman lafiya a shekara-shekara. To amman bai kebu daga irin ta’addancin da akan alakanata tsauraran kungiyoyin Islama a kasashen yamma ba.

XS
SM
MD
LG