Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Kunar Bakin Wake Ya Tarwatsa Kansa a Mogadishu


Mutum daya ya mutu, wasu biyu kuma suka jikkata bayan da wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a kusa da wani sansanin horon aikin soji na Turkiyya da Somaliya da ke Mogadishu a ranar Talata 23 ga watan Yuni, in ji shaidun gani da ido da jami'ai.

Lamarin ya faru ne a wajen wata makarantar firamare da sansanin ke tallafawa, a cewar wadanda suka shaida lamarin.

Maharin, wanda ya sanya da rigar nakiya, ya yi kokarin shiga wani layin sojoji a wajen sansanin da aka fi sani da TurkSom.

Jami'an rundunar sojan kasa na Somalia da ke gadin wurin, sun bude wuta kan mutumin bayan da suka ga take-takensa, amma mutumin ya tarwatsa kansa.

Wani farar hula da ke tsaye a wurin ya mutu, haka kuma wasu sojoji 2 sun jikkata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG