Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Dan Kunar Bakin Wake Ya Tayar Da Bam A Kofar Masallaci


Harin Kunar Bakin Wake Da Aka Kai Jami'ar Maiduguri

Wani ‘dan kunar bakin wake ya kashe kansa da wani matashi mai tsaron Masallaci a lokacin sallar Asuba a garin Maiduguri.

Da missalin karfe biyar da rabi ne ‘dan kunar bakin waken yayi kokarin kutsawa wani Masallaci a unguwar Dalori dake garin Maiduguri, sai dai bai sami sa’ar kutsawa ba sakamakon taka masa birki da wani matashi mai tsaron Masallacin yayi alokcin da ake sallar Asuba.

Nan take ‘dan kunar bakin waken ya tayar da bam din dake jikinsa ya kashe kansa da kuma matashin mai suna Salihu Ali, wanda aka ce ya kammala karatunsa na jami’a yana shirin tafiya yiwa ‘kasa hidima.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Borno, DSP Victor Isoko, ya aikawa manema labarai bayanai ta hanyar sadarwa, inda ya tabbatar da afkuwar lamarin da cewa yanzu haka komai ya koma dai dai.

Itama hukumar agajin gaggawa ta jihar Borno ta ziyarci wannan unguwa don ganewa idanunta yadda lamarin ya afku, wanda daga bisani ‘daya daga cikin ma’aikatan hukumar yayiwa manema labarai bayani, ya kuma yi kira ga al’umma da su rika sa ido don ganin an dakile faruwar ire-iren wadannan hare-hare.

A yan kwanakin nan dai ana ci gaba da samun matsalar hare-haren ‘yan kunar bakin wake da ma kai hare-hare a wasu hanyoyin dake fadin jihar Borno, inda ‘yan kungiyar Boko Haram suka fi karfi, wanda har rundunar sojan kasar ke ikirarin cewa sun riga sun ci ‘karfin ‘ya ‘yan kungiyar Boko Haram a yanzu.

Domin karin bayani ga rahotan Haruna Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG