Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Majalisar Dokokin Amurka Da Aka Harba Yana Cikin Mawuyacin Hali


Kakakin Majalisar Wakilai Paul Ryan yana magana bayan harin da wani ya kaiwa 'yan majalisa. June 14, 2017,

Dan Majilisar wakilai nan dan jamiyyar Republican da aka harba jiya laraba yana cikin wani mawuyacin hali bayan anyi masa aikin tiyata a asibitin nan dake Washington.

Dan Majilisar wakilai Steve Scalise daga jihar Louisiana shine mai tsawatarwa na majilisar wakilai, Ance yana cikin mawuyaci hali a asibitin MEDSTAR dake nan Washington DC bayan harbin da akayi masa a kwankwaso a lokacin da yake filin wasan kwallon hannu dake Alexandria, cikin jihar Viginia.

Ko baya ga wannan dan majilisar, haka kuma wadansu mutanen dake cikin filin wasan suma sun samu rauni iri daban-daban sakamakon wannan harbin da wani ya yi mashi a cikin filin wasan, inda dan majilisar dokokin ke atisayen wasan da za a gudanar yau alhamis domin bikin bada tallafi fadar gwamnatin kasar ta Amurka.

Shi dai wannan dan bindigar wani dan shekaru 66 da haihuwa ne, shima an jimasa rauni sakamakon harbinsa da yan sanda suka yi wanda daga bisani ya mutu.

Maharin dai yayi harbi ba kakkautawa ga mutanen dake cikin wannan filin wasan kafin ‘yan sanda su bude masa wuta.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG