Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dara Ta Ci Gida


Dan sanda yana aikinsa a birnin Los Angeles dake Jihar California, Amurka

An yi ma barayi sata a yayin da suka shiga wani kanti su na kokarin sato kaya daga ciki.

Dara ta ci gida ma wasu mutane biyu da ake zargi da yin sata a wani kanti, lokacin da suka zo tserewa daga wani wurin da suak yi kokarin sata, sai suka taras da cewa wani barawon ya shiga motarsu yayi musu kaf!

An kira 'yan sanda zuwa wani makeken kanti mai suna WinCo a garin Ogden dake Jihar Utah, inda aka tsare mutane biyu, Korin Vanhouten mai shekaru 47 da haihuwa da kuma Eldon Alexander mai shekaru 36 da haihuwa, ana zargin sun saci kayan shafe-shafe, da cakulet na kara kuzari da kuma batur. A bayan da 'yan sanda suka yi musu tambayoyi kuma ba a samu kayan a hannunsu ba, sai aka rubuta musu takardar tara bisa zargin sun yi kokarin satar kaya cikin kantin na WinCo.

Amma su na fitowa waje domin su yi tafiyarsu, sai suka samu cewa wani barawon, ko wasu barayin dabam, sun samu nasarar shiga cikin mota tare da yi musu sata mai yawa.

Abin ba a nan ya tsaya ba, domin kuwa Vanhouten da Alexander sun garzaya suka tare dan sandan da ya rubuta musu takardar tara ta kotu bisa zargin kokarin sata cikin kantin WinCo, suka fada masa cewa ai an yi musu sata.

Ashe lokacin da suek cikin WinCo suke kokarin sayaen kaya ciki ba tare da sun biya ba, wani ya labo ya fasa motarsu, ya cire rediyo da na'urar kara amon sauti, da ganga har ma da taba sigarin da suka bari ciki, duk an wawushe.

Kuma abin mamaki shi ne an fasa motar barayin aka yi musu sata a daidai lokacin da motar shi wannan dan sanda da ya yi musu tambayoyi ta ke ajiye a kusa da ta su.

Dara ta ci gida kam. Hausawa suka ce dan tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa ya kan doka.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG