Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DARAJAR NAIRA: SHUGABAR IMF ZA TA GANA DA BUHARI


Shugabar IMF, Christine Lagarde
Shugabar IMF, Christine Lagarde

A cigaba da fadi-tashin da ake yi na ganin an farfado da tattalin arzikin kasashe daban-daban wadanda faduwar farashin mai ya shafe su, jami'an Hukumar Bayar Da Lamuni Ta Duniya (IMF) za su yi tozali da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Yayin da tattalin arzikin Najeriya ke tangal-tangal sanadiyyar faduwar darajar Naira, wanda hakan kuma ke da nasaba da faduwar farashin mai a kasuwannin Duniya, Shugabar Hukumar Lamuni Ta Duniya IMF, Christine Lagarde, za ta ziyarci Najeriya, inda za ta gana da Shugaba Muhammadu Buhari don tattauna batutuwa masu alaka da tattalin arzikin Najeriya da ma na kasa da kasa.

Haka kuma da masu ganin za a tabo batun kara rage darajar Naira a wannan ziyarar wuni hudu da gaggan jami’an IMF za su kai Najeriya daga wannan Talatar. Rahotanni na nuna cewa Lagarde za ta tattauna da jami’an Najeriya da Kamaru a daidai lokacin da kasashen ke fuskantar durkushewar tattalin arziki sanadiyyar dalilai iri-iri.

Wani masanin tattalin arziki da ke kasuwar canji Abuja mai suna Alhaji Hashimu Muhammad y ace wannan ziyarar ta na da tasirin gaske ganin yadda tattalin arzikin yankin ke rarrafe. To saidai ya bayyana fargabar yiwuwa tawagar ta IMF ta gabatar da wani sharadin da ba zai dadada ma ‘yan Najeriya ba.

Ga wakilinmu Nasiru Adamu Elhikaya da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00
Shiga Kai Tsaye

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG