Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Darikar EYN Ta Koka Da Harin Dauki Daidai Da Ake Kaiwa Wasu Kauyuka A Adamawa


Wata motar da ta lalace a harin da aka kai kan wata unguwar Kiristoci ta Kano a Sabongari, a 2014.
Wata motar da ta lalace a harin da aka kai kan wata unguwar Kiristoci ta Kano a Sabongari, a 2014.

A dai dai lokacin da dakarun Najeriya ke kara kaimi wajen yaki da masu tada kayar baya na Boko Haram a wasu sasan arewa maso gabashin Najeriya,yanzu wata matsalar dai itace ta harin sari-ka noken da mayakan ke kaiwa wasu yankunnan da aka kwato daga hannun yan bindigan masu tada kayar bayan.

A wajen wani babban taron shekara-shekara na fastocin majami’ar Ekilisiyar 'Yan uwa ta Najeriya,EYN, da aka gudanar a shedikwatar majami’ar ta Najeriya a Kwarhi,shugaban cocin Ekilisiyar,Rabaran Joel Billi,yace yanzu haka al’ummomin da suka koma yankunan a kananan hukumomin Madagali,Chibok,da Gwoza na cikin yanayin zaman dar-dar sakamakon harin sari-ka,noke da garkuwa da mata da kananan yaran da mayakan Boko Haram keyi a wadannan yankuna.

Ya ce kamata yayi gwamnatin Najeriya ta dau mataki kan shawo kan wannan matsala da sake gina garuruwan da aka lalata ta yadda jama’a zasu samu natsuwa.

Haka nan kuma ,shugaban majami’ar ya bukaci gwamnatin jihar Adamawa data sake gina musu majami’un da masallatan da 'yan Boko Haram suka lalata musu a jihar ,kamar yadda gwamnatin jihar Borno ta yi.

Kimanin dai fastocin cocin 112 ne suka sami halartar taron na kasa baki daya,inda a karshe aka yiwa Najeriya addu’a ta musamman

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG