Wasu daruruwan matasa sun gudanar da zanga-zangar lumana a Minna babban birnin jihar Neja domin nuna bacin ransu akan yadda ‘yan bindiga ke yi wa jama’a kisan gilla a jihar, da ma wasu sassa a Arewacin Najeriya.
Masu zanga-zangar da suka sanya bakaken tufafi sun isa fadar mai martaba Sarkin Minna Dr. Umar Faruk Bahago, suka mika masa wata takardar koke zuwa ga gwamnatin Najeriya akan wannan bala’i na kisan jama’a.
Shugaban kungiyar kwadagon jihar Neja Kwamred Yakubu Garba wanda ya jagoranci zanga zangar, ya ce daukar matakin ya zama tilas domin al’ummar Arewacin kasar na cikin tashin hankali.
Shugabannin kungiyoyi daban daban ne a cikin wadanda suka gudanar da zanga-zangar.
Bayan da ya karbi sakon matasan masu zanga-zanga, mai marataba Sarkin Minna Dr. Umar Faruk Bahago ya ce, duk da yake ya san gwamnati na iya kokarin shawo kan matsalar tsaron kasar, amma zai mika sakon matasan ga gwamnatin.
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari.
Facebook Forum