Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutum 5,623 Sun Warke Daga Cutar COVID-19 a Najeriya Ya Zuwa Yanzu


Sabbin alkaluman da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya ta fitar sun nuna cewa karin daruruwan mutane sun kamu da cutar COVID-19.

A cewar hukumar, mutum 490 ne cutar ta harba wanda hakan ya mayar da adadin mutanen da suka kamu da cutar a kasar zuwa 17,148.

Har yanzu jihar Legas ce ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar wadda coronavirus ke janyowa, inda yanzu ta sake samun mutum 142. Sai birnin tarayya Abuja da ke bin ta da mutum 60.

Sauran jihohin da aka samu karin wadanda suka kamu da cutar sun hada da Bayelsa inda aka samu 54, 39 a Rivers, 37 a Delta, 30 a Oyo, 26 a Kaduna, 23 a Imo, 19 a Enugu, 17 a Kwara, 11 a Gombe, 10 a Ondo, 8 a Bauchi, 7 a Ogun, 6 a Borno, 1 a Benue.

Hukumar ta kuma bayyana cewa mutum 5,623 suka warke daga cutar yayin da mutum 455 suka mutu a jihohi 35, ciki har da birnin tarayya Abuja.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG