Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daruruwan Mutane Da 'Yan bindiga Suka Tarwatsa Sun Cika Sansanin 'Yan gudun Hijira A Jihar Neja


Wasu 'yan gudun hijira a Najeriya

Daruruwan mutane da 'yan bindiga suka tarwatsa daga garuruwansu suka cika sansanin 'yan gudun hijira na garin Gwada ta yankin karamar hukumar Shiroro a jihar Nejan Najeriya.

Mutanen dai da suka hada mata da yara kanana da kuma maza masu yawan shekaru sun ce sun bar garuruwansu ne saboda neman tsira da rayukansu a sakamakon muggan hare-haren da wadan an 'yan bindiga ke kai masu babu kakkautawa.

Hon. Attahiru Adamu, wani kansila ne daga yankin karamar hukumar Muya, ya kuma ce a yanzu Gundumomi 7 na karamar ta Muya, babu kowa a cikin su.

Kungiyoyin matasa a yankin, na ci gaba da taimakawa 'yan gudun hijirar.

Daya daga cikin shugabannin matasan, injiniya Usman Baba ya ce kashi 60 na manoman yankin Shiroron 'yan bindiga sun raba su da muhallansu.

Hukumomi a jihar Nejan dai sun sha bayyana cewa suna iya kokarinsu wajan shawo kan lamarin da kuma taimakawa yan gudun hijirar, inji Malam Habibu Musa, wani jami’in hukumar ba da agaji ta Jihar Nejan, mai kula da sansanin gudun hijirar na garin Gwada.

Wannan dai duk yana zuwa ne bayan da shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya ba da umurnin cewa sojojin kasar su aukawa 'yan bindiga da suka addabi jihar Nejan.

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG