Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasan Arewacin Najeriya Sun Fara Kai wa ‘Yan Gudun Hijrar Zamfara Dauki


‘Yan Gudun Hijira
‘Yan Gudun Hijira

Wasu yan arewacin Najeriya ciki har da matasa da ke zaune a cikin kasar da ma mazauna kasashen wajen sun fara amfani da kafafen intanet wajen neman taimakon kudi, kayan abinci da sutura ga ‘yan gudun hijirar jihar Zamfara da suka rasa muhallansu sakamakon ayyukan 'yan bindiga.

Hauwa Mustapha Babura 'yar Najeriya mazauniyar jihar Missouri da ke Amurka ne ta fara jan ra’ayoyin 'yan arewacin Najeriya musamman matasa da su tashi tsaye wajen nemawa 'yan gudun hijirar Zamfara da sauran jihohin arewa maso yamma da gabas taimako don samar musu na kaiwa bakin salati.

Hauwa Babura ta kuma bukaci gwamnatin Najeriya da ta samar wa al’ummar arewacin kasar ababen more rayuwa da suka hada da kiwon lafiya a saukake ga talaka, tattalin arziki da zai taimakawa wa masu kanana da matsakaitan sana’o’i da dai sauransu.

A halin yanzu dai matasa a arewacin Najeriya sun fara amsa kiran don taimakawa 'yan gudun hijira inda wata fitacciya a kafaffen sada zumunta irin su Instagram, Zainab Tanko Yakasai, ke amfani da shafinta na Instagram wajen karbar tallafin kudi ga kungiyoyin tallafi don kaiwa jihar Zamfara da hare-haren 'yan bindiga ya yi sanadiyyar raba dubban mutane da muhallansu.

Daga cikin watan Oktobar shekarar 2021 da ta gabata ne matasan suka fara yin hobbasa wajen samar da ci gaba a arewacin Najeriya.

Kyaftin Ibrahim Sharrif na daga cikin matasan Najeriya da ke kan gaba wajen neman sauyi a yanayin rayuwa ga yan yankin arewa inda ya ci gaba da yin kira ga a mayar da hankali wajen koya wa matasa sana da bin diddigin ayyukansu don cimma nasara a bangaren samun ci gaba a arewa kaman sauran yankunan kasar.

Idan ana iya tunawa dai, a bayan-bayan nan hare-haren yan bindiga da ke ficewa daga dazukan cihar Zamfara ya yi kamari ne sakamakon fatattakar miyagun da rundunar sojin saman kasar ke yi.

Gwamnatin Najeriya dai ta sake jaddada kokarinta na kawo karshen matsalolin tsaro a arewacin kasar baki daya.

XS
SM
MD
LG