Accessibility links

Har ya zuwa safiyar asabar din nan, babu wani bayanin da aka samu na yawan macemace ko raunin da aka samu a sanadin wannan hari na cikin dare a Sabon Garin Yambula a yankin karamar hukumar Madagali

Har ya zuwa wannan asubahin, babu cikakken bayani na yawan hasarar rayuka ko raunin da aka samu a sanadin wani harin da 'yan bindigar da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka kai kan wani kauye mai suna Sabon Garin Yambula a yankin karamar hukumar Madagali ta Jihar Adamawa, cikin daren nan ba.

Wannan harin yana zuwa kasa da sa'o'i biyar kacal a bayan tashin wani bam a kan hanyar kauyen Takaskala, mai tazarar kilomita 20 daga garin Madagali, inda wasu rahotanni ke cewa mutane fiye da 10 suka mutu.

Mutanen yankin suka ce 'yan bindigar sun isa kauyen na Sabon Garin Yambula bayan isha'i su na bude wuta kan jama'a. Wasu majiyoyi sun ce an sanar da hukumomi tsaro kuma an tura sojoji zuwa can.

Sai dai kuma duk kokarin da wakilin Muryar Amurka, Ibrahim Abdulaziz, yayi domin jin ta bakin jami'an tsaro cikin daren nan, abin ya ci tura, don babu wanda ya amsa wayarsa.

Daya daga cikin shugabannin yankin karamar hukumar ta Madagali, Maina Ularamo, ya tabbatar da abkuwar wannan harin, ya kuma ce sun yi magana da jami'an tsaro wadanda suka ce su na kan hanyar zuwa wurin.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
XS
SM
MD
LG