Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Datti Ahmed Ya Bayyana Dalilan Da Aka Tsaida Shi Mataimakin Peter Obi A Labour Party


Prof. Datti Baba Ahmed

Shugaban jami’an Baze kuma masani a fannin ilimi da tattalin arziki ya ce jam’iyyar Labour Party ta duba cancantarsa ta bangaren yawan shekaru, kwarewa a bangaren ilimi, aikin fadakar da al’umma da kuma sanin tattalin arziki ne kafin ta tuntube shi ta bashi wannan takarar mataimakin shugaban kasar.

Datti Baba Ahmed ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da Muryar Amurka a birnin Abuja.

Tsohon dan majalisar dattawa da na wakilai da ya wakilci jihar Kaduna a tarayyar Najeriya ya ce daya daga cikin abubuwan da suka jawo ra’ayinshi ga amincewa da matsayin da aka bashi a jam’iyyar LP shi ne a lokacin da ya ambaci cewa fadin kasar dake yankin arewa shi ne man Najeriya ba man da aka sani a kudu ba.

A cewar Datti, birane irin su Kaduna da Kano kadai sun isa a ce suna tantance abubuwan da aka noma a sarrafa su lamarin da zai iya zama wata babbar hanya ta bunkasa samun kudadden shiga a cikin gida.

Muna san mu tsaida faduwar naira, saboda a matsayin shugaban kasa idan kana da ‘yan uwa da ba sa amfana da faduwar darajar Naira, naira zata tsaya daidai, in ji Datti Ahmed.

Haka kuma, Datti ya ce muddin shugaba baya sata yana da hujjar hukunta ko waye ke yi.

Ku saurari karin bayani cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

XS
SM
MD
LG