Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Davido Zai Yi Wasa Na Farko A Najeriya Tun Bayan Rasuwar Dansa


Davido a lokacin da ya ke karbar lambar yabon BET
Davido a lokacin da ya ke karbar lambar yabon BET

Davido zai yi amfani da wasan wajen tallata sabon kundin wakokinsa da ya yi wa take da “Timeless.”

Fitaccen mawakin Afrobeat a Najeriya David Adeleke wanda aka fi sani da Davido, zai gwangwaje a filin wasa na Tafawa Balewa Sqaure (TBS) da ke Legas a Najeriya.

Wannan shi ne wasan Davido na farko da zai yi tun bayan rasuwar dansa Ifeanyi a bara.

Davido zai yi amfani da wasan wajen tallata sabon kundin wakokinsa da ya yi wa take da “Timeless.”

A ranar Lahadi 23 ga watan Afrilun 2023 wasan zai gudana a filin na TBS mai daukan mutum 50,000 a jihar ta Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Tun bayan da ya saki kundin a watan Maris, wakokin kundin ke ta tashe a dandalin sauraren wakoki na yanar gizo a Najeriya.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG