Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Reno Omokri Ya Tofa Albarkacin Bakinsa Kan Tara Wa Davido Kudi


Davido (Hoto: Davido Instagram Courtesy - Fortune)
Davido (Hoto: Davido Instagram Courtesy - Fortune)

Sanannen mawakin Najeriya David Adeleke wanda aka fi sani da Davido ya ce zai ba gidajen marayu a fadin Najeriya naira miliyan 200 da abokan aiki da masoyansa suka tara mashi.

Mawakin na Hiphop ya sanar da wannan albishir din ne a shafinsa na Instagram ranar Asabar.

Ya ce zai kara miliyan 50 daga aljihunsa akan miliyan 200 da aka tara mashi su zama miliyan 250 don kokarin taimaka wa marasa karfi.

Bayan da ya gode wa wadanda suka tara mashi kudin, ya bayyana cewa ya dade yana sha’awar yi wa mabukata da marasa karfi alheri.

Wannan batu dai ya janyo mabambantan ra’ayoyi a tsakanin ‘yan Najeriya ciki har da Reno Omokri, hadimin tsohon shugaba Goodluck Jonathan a lokacin mulkinsa, yana mai cewa Davido ya fi wadanda suka tara masa kudi hikima. Saboda ya fahimci tasirin yin hakan a addini da kuma hanyoyin Allah.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG