Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daya Daga Cikin Iyayen Daliban da Aka Sace Ya Kwanta Dama


Wasu iyayen daliban Chibok da aka sace.
Wasu iyayen daliban Chibok da aka sace.

Bayan makonni biyar da aka sace dalibai mata kusan su dari uku daga makarantar 'yan mata dake Chibok cikin jihar Borno, daya daga cikin iyayen daliban dake da 'ya'ya biyu ya samu bugun zuciya ya rasu.

A wani abun tausayi da juyayi daya daga cikin iyayen 'yan matan makarantar sakandare ta Chibok da 'yan Boko Haram suka sace ya samu bugun zuciya kuma ya rasu. Shi wannan mahaifin yana da 'ya'ya biyu cikin yaran da kungiyar ta'adancin nan ke rike da su.

Ranar Lahadin da ta gabata daya daga cikin iyayen yaran ya rasu sakamakon bugun zuciya da ya kamu da shi.Tun lokacin da aka sace 'yan matan wasu alamura da dama suka faru wadanda suka hada da mutuwar wannan mahaifin.

Kungiyoyi masu karfi da masu zaman kansu a ciki da wajen Najeriya sun yi zanga zanga akan sace yaran. Haka ma gwamnatocin duniya gaba daya suka yi tur da lamarin yayin da wasu kasashe suka kawowa kasar Najeriya doki domin a gama da kungiyar Boko Haram.

Mr. James Yemen mazaunin karamar hukumar Chibok shi ne danuwan mutumin da ya rasu yace rashin ganin 'ya'yansa mata guda biyu ya tayar masa da hankali matuka. Lamarin da ya kara tada masa da hankali shi ne rashin ganin 'ya'yansa a cikin bidiyon da kungiyar Boko Haram ta fitar kwanaki. Marigayin yana da 'ya'ya takwas da suka hada da 'yan matan biyu da aka sace.

Mr James Yemen yace rashin labarin yaran ya sasu cikin tunane kullum. Sun rasa abun da zasu yi. Yace danuwan nasa yana cikin tunane koyaushe hatta abinci ma baya ci. Wasu da yawa idan an basu abinci ma ba zasu ci ba sabili da zurfin tunane.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG