Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Dimokradiyya Ta Yi Nasara', Biden Ya Lashen Kuri'un Kwalejin Zabe


Zababben shugaban kasa Joe Biden
Zababben shugaban kasa Joe Biden

Zababbaen shugaban Amurka Joe Biden ya ce “a gwagwarmayar kare Amurka, Dimokradiyya ta yi nasara,” a jawabin da yayi ranar Litinin, jim kadan bayan da wakilai na musamman suka tabbatar da zaben sa a matsayin shugaban kasa.shugabancinsa. 

Yayin da yake kira ga Amurka cewa yanzu lokacin na “Hada kai, da dinke baraka,” a karon farko Biden ya fito fili ya yi Allah wadai da yunkurin shugaban kasa Donald Trump da abokanansa na juya sakamakon zabe, abin da ya kwatanta a matsayin “Cin zarafin da ba’a taba yi wa dimokradiyyarmu ba.”

Ba wani amfani da iko da ba bisa ka’ida ba, da zai iya hana mika mulki cikin lumana, in ji Biden, sa’o’i kadan bayan da masu jefa kuri’a na kwalejin zaben suka kada kuri’unsu a kowace jiha da kuma Gundumar Columbia.

“Mu mutane mun kada kuri’unmu, mun yi imani da hukumomin da suka gudanar, mutuncin zabubbukanmu na nan daram,” Biden ya ce a cikin jawabin da ya gabatar a garin Wilmington na jihar Delaware.

Masu zabe a ranar Litinin sun bai wa Biden kuri’a 306 shi kuwa shugaban kasa na kai Trump ya samu kuri’a 232, cikin kwanciyar hankali, adadin da ya dara 270 da ake bukata a zaben.

Adadin kuri’a 306 da Biden ya samu sun yi daidai da abin da Trump ya samu shekaru hudu da suka wuce a lokacin da ya kayar da ‘yar takarar jam’iyyar Demokrat Hillary Clinton.

“A lokacin, shugaba Trump ya kwatanta sakamakon kwalejin zabensa da gagarumin rinjaye,” in ji Biden. “bisa wannan ikrari nasa, wadannan lambobi sun nuna gagarumar nasara a wancan lokacin, kuma ina ga bisa girmamawa, haka ya kamata ya zama a yanzu.”

Tsohon shugaban kasar, a lokacin da yake jawabi a garin Wilmington, ya ce “Idan wani bai sani ba, mun sani yanzu. Abin da yake kasan zuciyar Amurkawa shi ne, Dimokradiyya.”

Trump ya ki ya amincewa da shan kaye, yana ikirari ba tare da hujja ba cewa, zaben an yi magudi kuma Biden zai kasance haramtaccen shugaban kasa.

Shi dai Trump bai yi maza ya mayar da martani bisa wannan kalamai na Biden ba, amma a ranar Lahadi ya shiga shafin Twitter inda y ace, “jihohin da aka yi gwagwagwa wadanda aka tafka magudi a dukkaninsu, BA ZA SU IYA HALALTA wadannan kuri’u ba a matsayin cikakku masu sahihanci ba tare da an an tafka kuren da ake hukunci akansa ba.”

Kamfen din shugaba Trump sun shigar da kararraki da dama, wadanda alkalai suka yi watsi da su.

Sai dai,a ranar Litinin, Sanata John Thune, wanda shi ne na biyu cikin manyan sanatocin na jam’iyyar Republican, y ace. “lokaci ya yi da za a kara gaba,” sannan y ace da za ran Biden ya lashe kuri’un kwaleji da suka haura 270, shi ne zai zama zababben shugaban kasa kamar yadda Reuters suka ruwaito ta ruwaito.

XS
SM
MD
LG