Accessibility links

A yayin da ake ta shirye shiryen rantsar da sabuwar gwamnati a Najeriya, jam'iyar PDP wadda ta sha kaye a babban zaben da ya gabata na fama ne da wata sabuwar danbarwa.

A kwanakin baya Alhaji Ahmed Adamu Mu’azu na jam’iyar PDP ya sha kuda daga Shugaba Goodluck Jonathan mai barin gado da kuma wasu ‘ya’yan jam’iyar, wanda a cewar su shi ke canza kida da rawar jam’iyar wato mai canza sabon takun jam’iya zuwa ga nasara. Sai dai da alama wannan karon nasarar bata samu ba.

‘ya’yan jam’iyar a yanzu haka dai suna ta kushe juna da dora wa juna alhakin faduwar jam’iyar babban zaben kasar da ya gabata ne wanda har ya kaiga sa Alhaji Ahmed Adamu Mu’azu yin murabus daga jam’iyar ta PDP.

Wasu daga cikin jigogin jam’iyar cewa suke cin karo da bukatun shugaba Jonathan yayi sanadiyyar hakan, jam’iyar dai a halin yanzu tana fafutukar neman gamaiyya ne da wasu jam’iyu kamar jam’iyar AFGA, da jam’iyar LABOUR, da kuma sauran su, dan karfafa adawa da jam’iyar APC ko da hakan bazai kaiga canza sunan jam’iyar ba.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG