Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Samar Da Wutar Lantarki A Yankunan Da Boko Haram Suka Lalata A Najeriya


Kayayyakin Samar Da Wutar Lantarki A Najeriya

Yayin da dakarun Najeriya ke ci gaba da kwato dukkanin yankunan dake hannun mayakan Boko Haram a jihohin Adamawa, Borno da kuma jihar Yobe, yanzu haka hukumar samar da wutar lantarki ta fara samar da wuta a wasu yankunan da aka kwato.

Wannan yunkuri na mayar wutar lantarkin dai ya ko biyo bayan nasarar da ake samu a yaki da masu tada kayar baya na Boko Haram, wanda kawo yanzu aka kwato wasu yankunan da a baya suka fada hannun yan Boko Haram.

To sai dai kuma wannan na zuwa ne yayin da masu amfani da wutar lantarkin ke kokawa kan tsadar kudin wutar da suke biya a yanzu.

Alkalumman kamfanin samar da wutan lantarki shiyar Yola na na nuni da cewa na’urorin samar da wutar lantarki masu yawa ne ‘yan Boko Haram suka lalata, baya ga ofisoshinsu da aka kona, lamarin da ya jawo katsewar wutar lantarki a yankunan.

Yanzu dai da aka samu kwanciyar hankali, kamfanin samar da wutar lantarki shiyar Yola da ta kunshi jahohin Adamawa da Borno da Yobe da kuma jihar Taraba tuni dai ta fara gudanar da ayyukanta a wasu yankunan da aka kwato.

Injiniya Umar Al-Mustapha dake zama babban daraktan kamfanin samar da wutar lantarki na wannan shiyar, YEDC, yace guraren da aka samar da wutar lantarkin sun hada da garin Mubi dake zama cibiyar kasuwancin Arewacin jihar Adamawa, da Maiduguri da wasu yankuna na jihar Yobe.

To sai dai kuma, wannan na zuwa ne yayin da cikin kwanakin nan ake samun karancin wutar lantarkin da kuma dan karin kudaden da ake karba daga hannun jama’a, koda yake babban daraktan kamfanin YEDC, Injiniya Umar Al-Mustapha yace matsalar ba daga garesu bane.

Manazarta na ganin cewa Najeriya na da sauran aiki a fanin samar da wuta duk kuwa da mayar da harkar hannun ‘yan kasuwa, domin kasar na samar da abin da bai kai Megawatt Dubu shida ba ga al'umma miliyan 170, idan aka kwatanta da Afrika ta Kudu mai samar da Megawatt na wuta dubu 50 ga al'ummarta mai yawan mutane miliyan 40, abin da ya sa kwarraru ke bayyana bukatar rungumar tsarin samar da wutar lantarki ta hanyar da ake sabuntawa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG