Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dole ne 'Yan Najeriya su Natsu su Bi Doka


Majalisar Dakokin Najeriya

'Yan Najeriya da shuwagabanin Najeriya sun yarda da damokradiya,kuma mun rungumi damokradiya

Najeriya yanzu ta kwashe Shekaru goma sha hudu ta mulkin damkradiya, wanda masana kamar farfesa Umar Pate na ganin cewa yafi mulkin danniya.

Ya furta hakan ne a hiran da suka yi da wakilin muryar Amurka, Nasiru Adamu Elhikaya, a Abuja.

Farfesa Umar Pate yace”a Najeriya kowa ya san damokradiyar da mukeyi gurguwar damokradiya ce saboda irin yanda muka kirkiro matsaloli muka makalawa siyasarmu, idan ka lura zaka ga lalle’yan Najeriya da shuwagabanin Najeriya sun yarda da damokradiya, kuma mun rungumi damokradiya.”

Ya kara da cewa “abu daya da muka kasa yi shine daukan halin da’a na damokradiya kaga idan kana damokradiya dole akwai alamar gaskiya a ciki dole kuma kabi dokoki dole kuma ka bi tsarin da aka shifida ko da dadi ko ba dadi, amma mu idan ka lura saboda kaucewar shugabancin ko kuma nakasar shugabanci, a matsayi taraiya,jihohi ko kuma kananan hukumomi akwai matsaloli, na biyu cin hanci,rashawa da rashin bin tsari irin na aiki shi kuma ya zama mana sankara a irin siyasar da muke tare dashi.”

Yace dole ne mu natsu mu koyi darasi mu san cewa damokradiyar nan bawai sake bane kawai ake yinsa damokradiya yana da dakoki kuma dole mu natsu mu bi dokoki nan.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG