Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Yara ta Duniya ta Zama ranar Addu'o'i a Jihar Neja


Iyayen da ‘yan uwan ‘yan matan da aka sace.
Iyayen da ‘yan uwan ‘yan matan da aka sace.

Maimakon yin bikin ranar yara ta duniya kamar yadda aka saba kowace shekara gwamnatin jihar Neja ta mayarda ranar ranar addu'o'i sabili da yaran da kungiyar Boko Haram ta rutsa da su da kuma 'yan mata fiye da dari biyu da take garkuwa da su.

A wani abun da ba'a saba gani ba gwamnatin jihar Neja ta mayar da ranar yara ta duniya ranar addu'o'i na musamman sabili da daliban Chibok da 'yan kungiyar Boko Haram ke garkuwa da su.

Gwamnatin ta tara yara Musulmai da Kirista domin su yi addu'a ta musamman Ubangiji Ya sa a sako daliban da ake garkuwa da su. Gwamnatin jihar da shirin cire tallafin man fetur ko SURE-P suka dauki nauyin shiryawa da gudanar da addu'o'in.

Alhaji Hassan Nuhu babban daraktan shirin SURE-P ya yi karin bayani inda yace mai girma gwamnan jihar Dr. Muazu Babangida Aliyu yana ganin a ranar irin ta jiya a tara yara da manyan shugabannin addinai su yi addu'o'i na musamman domin Allah Ya kubutar da yaran da 'yan Boko Haram suka yi garkuwa da su. Kuma haka aka yi inda aka sa yara Musulmai da Kirista suka yi addu'o'i.

Alhaji Shehu Haruna kwamishanan kula da harkokin addinai na jihar Neja ya bayyana dalilin sa yara su yi addua.Yace Allah yana karbar addu'ar yara domin basu da zunubi. Addu'ar ta neman Allah Ya taimaka yaran da aka sace su fito.

Batun cewa ko babu wata dabara da ta ragewa gwamnatin Najeriya sai komawa ga addu'a, Alhaji Ahmed Isa Ibeto mukaddashin gwamnan jihar wanda kuma shi ne ya karanta jawabin shugaban kasa Goodluck Jonathan yace gwamnati tana da dabaru amma kuma addinai sun nuna a roki Ubangiji.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00
Shiga Kai Tsaye

Labarai masu alaka

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG