WASHINGTON, DC —
A wannan shirin, mun yi hira da kwamishinar ma'aikatar mata ta jihar Kano dagane da batun Ahmed Aminu matashin da mahaifinsa ya kulle a gareji na tsawon shekaru bakwai.
A cikin hirarta da shirin Domin Iyali, ta bayyana matakan da gwamnati da kuma asibitin da ake kula da shi suke dauka domin ganin an bashi cikakkar kulawa.
Saurari cikakken bayanin da ta yi wa Mahmud Ibrahim Kwari
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.