Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Hira Da Barrista Badiha Abdullahi Mu'azu Kan Matsalar Fyade A Najeriya- Yuli 23, 2020


Alheri Grace Abdu

Matsalar fyade da ta ke ci gaba da zama babban kalubale a Najeriya ta nakara daukar hankalin al’umma a ciki da wajen kasar. Lamarin da ya kai ga kungiyoyin mata da suka hada da matan gwamnoni da kwamishinonin ma’aikatun kula da harkokin mata, jagorantar gangamin neman ganin hukumomi sun dauki kwararan matakan shawo kan wannan matsala da ke nema ta zama bala’i.

A ci gaba da haska fitila kan mummunar dabi’ar, yau shirin domin iyali ya yi hira da barrista Badiha Abdullahi Mu'azu wadda ta jima tana bin diddigin wannan batu a kotu, ta kuma bayyana wa wakiliyarmu Baraka Bashir cewa, duk da ganganin da ake yi, babu alamar sauki

Saurari cikakken shirin

FYADE: Hira da Barrister Badiha Abdullahi Mu'azu :10:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:08 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG