Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Hira da Rabi Salisu Ibrahim Kan Matsalar Fyade A Najeriya- Yuli 16, 2020


Alheri Grace Abdu

A ci gaba da haska fitila kan mummunar dabi’ar nan ta fyade da ta buwayi al’umma a Najeriya da ya sa kungiyoyin mata suka shiga tuntuba da zanga zanga, da nufin jawo hankalin hukumomi su dauki mataki, yau shirin domin iyali ya yi hira da Rabi Salisu Ibrahim wadda aka aka rika yayata bayanai da ta yi a da bacin zuciya a shafukan sada zumunta, kan yadda aka bata rayuwar wata yarinya ‘yar shekaru goma da maza da dama suka yi ta yi wa fyade, wadansu har da yi mata fyaden taron dangi.

Saurari bayanin rahotannin da suka samu na iri-irin wadannan matsalolin a cikin hirar Hajiya Rabi da wakilinmu Isa Lawal Ikara.

Hira da Rabi Salisu Ibrahim kan matsalar fyade-10:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:59 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG