Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Tattaunawa Kan Cin Zarafin Mata A Gidan Aure-Kashi Na Biyu-Mayu 26, 2022


Alheri Grace Abdu

A ci gaba da nazari kan matsalar Cin zarafin iyali ya ke kara ci kamar wutar daji a Najeriya, duk da gangamin da ake yi da kuma tada tsimin jama’a da nufin shawo kan matsalar. A yau ma muna tare da Ministar harkokin mata a Najeriya Pauline Tallen, da kuma Mustapha Suleiman shugaban wata kungiyar matasa da ake kira “Youth Assembly Of Nigeria” wadanda suka bakunci shirin sakamakon mutuwar wata fitacciyar mawakiya Osinachi Nwachuku a birnin tarayya Abuja, da ake zargin maigidanta da sanadin mutuwar ta. Minista Pauline Tallen tana bayanin kan mafita tsakanin ma’aurata lokaci ya kwace mana, inda kuma mu ka dora ke nan yau.

Saurari cikakken shirin cikin sauti:

DOMIN IYALI: Tattaunawa Kan Cin Zarafin Mata A Gidan Aure-Kashi Na Daya-Kashi Na Biyu-10:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:19 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG