Idan kuna biye da mu, shirin Domin Iyali ya karbi bakuncin, Tsohuwar Ministar mata Aisha Isma’il da Barrista Hassana Ayuba Mairiga, da kuma ‘yar gwaggwarmaya Balaraba Abdullahi da ke nazari kan watsi da kudurin da zai ba mata damar cimma burinsu na samun kashi talatin da biyar cikin dari na guraban siyasa a kasar da majalisar dokokin kasar ta yi. Hajiya Aisha Isma’il na bayani kan dalilan da ya sa ‘ majalisar da maza su ka mamaye ta yi watsi da batun lokaci ya kwace mana, inda za mu dora ke nan yau a tattaunawar da wakiliyarmu Madina Dauda ta jagoranta.
Saurari cikakken shirin:
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.