Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump Zai Gana Da Shugaban Kasar Mexico


Donald Trump da Mike Pence

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyar Republican Donald Trump zai gana da shugaban kasar Mexico Entrique Pena Nieto yau Laraba, kafin jawabin da zai gabatar inda zai bayyana tsare tsarensa na shige da fice.

Donalt Trump ya yi ta nanata niyarsa ta gina ganuwa kan iyakar Amurka da Mexico, kuma gwamnatin Mexico ce zata biya kudin ginin. Neito yana cikin jami’an kasar Mexico da suka ce bata sabuwa.

Ofishin Nieto ya fada a shafinsa na twitter cewa, shugaban kasar Mexico ya gayyaci Trump da ‘yar takarar jam’iyar Democrat Hillary Clinton domin tattauna dangantaka tsakanin kasashen dake makwabtaka da juna. Babu wani bayani daga ofishin yakin neman zaben Clinton kan ko ta karbi goron gayyatar ko babu.

Trump zai bayyana shirinsa na shige da fice ne gobe a jihar Arizona dake kan iyaka a kudu maso yammacin Amurka, inda aka shafe shekaru ana fama da kwararar bakin haure.

XS
SM
MD
LG