Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump Yayi Kira Da A Maida Iran Saniyar Ware


 Donald Trump Yayin Da Yake Jawabin A Taron MDD
Donald Trump Yayin Da Yake Jawabin A Taron MDD

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya da suke hallartar taron Kolin MDD cewa, su maida gwamnatin Iran saniyar ware muddun taci gaba da cin zali, yayinda ya zargi shugabannin Iran da haddasa rudani da mutuwa da kuma barna.”

Trump yace, shugabannin Iran “basu mutunta makwabtansu ko kan iyakokinsu ko sauran kasashe. A maimakon haka shugabannin Iran suna azurta kansu da dukiyar kasar, yayinda kuma suke haddasa tashin hankali a gabas ta tsakiya da kuma wadansu yankuna dake nesa.

Trump ya jadada cewa, yarjejeniyar da aka cimma a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar zamanin mulkin Obama na kawo karshen ayyukan nukiliyan Iran, wanda ya janye, wata garabasa ce kawai shugabannin Iran suka samu, da ya bada damar kara karfin ayyukan sojin kasar Iran da kimanin kashi arba’in cikin dari, da kuma daukar nauyin ayyukan ta’addanci da aikata ta’assa a Syria da kuma Yemen.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG