Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dr. Kabir Mato Ya Bayar da Dalilan da Su ka Haifar da Jita-Jitar Juyin Mulki


Babban hafsan hafsoshin sojojin Najeriya, Air Marshal Alex Badeh wanda ya karyata jita-jitar juyin mulkin.
Babban hafsan hafsoshin sojojin Najeriya, Air Marshal Alex Badeh wanda ya karyata jita-jitar juyin mulkin.

Duk da shashantar da maganar jita-jitar juyin mulkin da sojoji suka yi, Dr. Kabir Mato ya ce akwai abubuwan da suka sa mutane yin tunanin hakan.

Hafsan hafsoshin sojojin Najeriya ya fito ranar Laraba yayi watsi da jita-jitar cewa akwai yiwuwar sojoji za su yi juyi mulki a Najeriya, kasar da ta fi yawan jama'a a nahiyar afirka, wadda kuma yanzu haka ta ke fama da masifar ta'addancin kungiyar Boko Haram.

Babban hafsan Alex Badeh ya ce don me mutane su ke yin mugun alkaba'i, ya ce a gayawa masu yada jita-jitar ba za su yi juyin mulkin ba. Kuma ya kara da cewa masu yada jita-jitar juyin mulki, lallai ba a cikin Najeriya su ke ba.

Amma a tattaunawar Babban Editan Sashen Hausa Aliyu Mustaphan Sokoto, da masanin ilimin kimiyyar siyasa Dr. Kabir Mato na jami'ar Abuja, masanin ya fayyace batun dalla-dalla, kuma ya lissafa wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya yanzu haka, wadanda masu yada jita-jitar suka gani, kuma su ka yi amfani da su a matsayin dalilai.
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:23 0:00
Shiga Kai Tsaye

Air Chief Marshal Alex Badeh ya karyata maganar cewa sojoji za su kwace mulki, sannan ya bayyana cewa jita-jitar yin juyin mulkin abun mamaki ne, kuma ya ce sojojin Najeriya sun san kan aikin su, kuma su na kaunar kasar su.

Idan ba a manta ba dai a 'yan kwanakin da suka wuce sojojin Najeriya su ka kaddamar da wani tsattsauran mataki akan jaridun d ake wallafawa a kasar saboda dalilan tsaro, acewar sojojin, amma wasu kafofin yada labaran kasar sun ce gwamnatin Najeriya na fakewa ne da guzuma ta harbi karsana, wato kokari ta ke yi ta hana bakin magana, ta tauye 'yancin furta albarkacin baki ta hanyar rabewa da tsaro.
XS
SM
MD
LG