Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban mutane sun halarci gamgamin goyon bayan Putin a Rasha


Wani mutum rike da rubutu dake nuna goyon bayan Putin
Wani mutum rike da rubutu dake nuna goyon bayan Putin

Dubban mutane a birane dabam dabam na kasar Rasha sun yi gangami yau asabar na nuna goyon bayan Firai Minista Vladimir Putin a niyarshi da takarar shugaban kasa.

Dubban mutane a birane dabam dabam na kasar Rasha sun yi gangami yau asabar na nuna goyon bayan Firai Minista Vladimir Putin a niyarshi da takarar shugaban kasa.

An yi gangami mafi girma a St Petersburg, inda ‘yan sanda suka yi kiyasin cewa, kimanin mutane dubu sittin suka taru domin nuna goyon bayan Mr. Putin.

Daya daga cikin magoya bayan Putin, Valentina Taran ta musanta cewa an tilasta jama’a halartar gangamin. Tace, “muna goyon bayan Mr. Putin da ayyukanshi, kuma zamu zabi Vladimir Vladimirocich Putin. A gaskiya ma a tashar talabijin muka ji labarin gangamin.”

Masu zanga zanga da dama sun yi kokarin yin amfani da gangamin wajen nuna kin jinin Mr. Putin da tsare tsarenshi. Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya laburta cewa an kama masu zanga zangar kin jinin Mr. Putin guda biyu.

Dubban mutane kuma sun halarci gangamin nuna goyon bayan Mr. Putin a Nizhny Novgorod, da Stravopol , da Vladivostok da kuma Volgograd.

Mr. Putin ya zama Firai Minista ne bayan shugabancin kasar daga shekara ta dubu biyu zuwa dubu biyu da takwas. A watan Satumba bara

ya sanar da niyarshi da sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaben da za a gudanar cikin watan Maris, da zai sa su yi musayar matsayi da shugaba Dmitry Medvedev.

Binciken ra’ayoyin jama’a na nuni da cewa, yana yiwuwa ya lashe zaben, sai dai takararshi ta haifar da kazamar zanga zanga irin wadda ba a taba gani bat un bayan rugujewar tsohuwar gwamnatin Sobiyet.

A farkon wannan watan kafofin sadarwar kasar Rasha suka bada rahoton cewa, kimanin mutane dubu talatin da biyar suka shiga zanga zangar kin jinin Mr. Putin a birnin Moscow ko da yake shugabannin hamayyar sun bayyana cewa adadin mutanen ya haura haka nesa.

XS
SM
MD
LG