Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a binne Whitney Houston yau a jihar New Jersey


Akwatin gawar Whitney Houston

Yau Lahadi za a yiwa fitattar mawakiyar nan Whitney Houston kusheyi a jihar ta New Jersey.

Yau Lahadi za a yiwa fitattar mawakiyar nan Whitney Houston kusheyi a jihar ta New Jersey.

Hukumomi sun ce za a tsawata tsaro a ciki da kuma kewayen makabartar, bisa kyautata zaton cewa, masoyanta zasu yi dafifi a wurin da nufin yi mata rakiyar girmamawa ta karshe.

Za a binne Houston ne a gangan mahaifinta John Russel Houston Jr, a makabartar Fairview dake Westfield.

Dangin mawakiyar ne kadai zasu ga yadda aka binneta ba za a yayata a kafofin sadarwar internet da kuma talabijin kamar yadda aka yayata jana’izar da aka shirya ta karramata jiya asabar ba.

Fitattatu a fannoni dabam dabam da suka hada da mawaka ne suka halarci jana’izar girmamawa da aka yi ta karshe jiya asabar a majami’ar da ta girma a ciki dake Newark, jihar New Jersey inda Houston ta yi waka a kwaya tana karama. Ma’abotanta sun nuna mata kauna ta wajen ajiye daruruwan balon balo da furanni da katuna a kofar majami’ar.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG