Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MLK: Dubban Mutane Sun Hallara a Washington a Zagayowar Ranar Jawabin Martin Luther King


Dubban mutanen da su ka hallara a Washington a zagayowar Ranar Jawabin Martin Luther King
Dubban mutanen da su ka hallara a Washington a zagayowar Ranar Jawabin Martin Luther King

Dubun dubatan mutane ne su ka taro a Washington, babban birnin Amurka jiya Asabar don bukin zagayowar ranar jawabin Rev. Martin Luther King Jr.

Dubun dubatan mutane sun hallara a birnin Washington jiya Asabar don tuna jawabin Reverend Martin Luther King Jr mai taken “I Have A Dream” wato “Ina Wani Mafarki,” wanda jawabi ne na rajin kare hakkin dan adam da ya yi shekaru 50 da su ka gabata.

A 1963 Bakaken Fatan Amurka na kokarin jure banbancin launin fatan da su ke fuskanta, wanda ya takaita ‘yancin kada kuri’a ga Bakake a sassan Amurka; ya hana su samin ayyukan yi masu kyau sannan ya jefa da yawansu cikin talauci.

Jawabin na Mr King ya janyo macin da mutane 250,000, wanda ya nuna yadda ake ta kara samun mutane masu ra’ayin gwagwarmayar siyasa cikin lumana, wanda sannu a hankali hakan ya sa aka samar da sabbin dokoki da su ka tabbatar da ‘yancin ‘yan kasa ga Bakake da sauran mutane.

Yau shekaru 50 kenan sai gashi Attoni-Janar din Amurka Eric Holder ya shaida ma masu kwaikwayan wancan macin cewa ‘yan gwagwarmayar tabbatar da ‘yancin dan kasa da su ka gabata ne su ka sa ya zama Bakar Fatan Amurka na farko da ya zama Shugaban Ma’aikatar Shari’ar. Y ace amma har yanzu da sauran aiki don kare ‘yancin yin zabe ga Bakaken fata da kuma samar da irin wannan ‘yancin ga sauran al’ummomi irinsu Hispaniyawa da ‘yan luwadi.

Dadadden dan gwagwarmayar kare hakkin dan adam Reverend Jesse Jackson y ace shekaru 50 bayan wancan jawabin na Mr King, “mun samu ‘yanci to amma ba daidai mu ke ba” sannan ya yi kira ga masu sauraronsu cewa su cigaba da irin mafarkin da King ya yi, su raya manufar, da kuma kyakkyawan zato.

Shi da ya ke jawabi ga taron, jigon rajin kare ‘yancin dan adam Julian Bond, yace alkaluman tattalin arziki sun nuna cewa har yanzu fa Bakake na can bayan Turawa. Ya yi Allah wadai da matsayin da Kotun Kolin Amurka ta dauka a baya bayan nan da cewa ya yi illa ga ‘yancin zaben da aka yi gwagwarmaya da mutuwa a kansa.
XS
SM
MD
LG