Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban Mutane Sun Je Yi Wa Marigayiya Sarauniya Elizabeth Ganin Karshe


Britain mourns Queen Elizabeth
Britain mourns Queen Elizabeth

Yayin da fadar masarautar Birtaniyya ta fitar da tsarin abubuwa da za a yi har zuwa lokacin jana'izar Sarauniya Elizabeth ta biyu, dubban mutane sun ja layi tun daga daren Laraba har zuwa wayewar garin Alhamis don ganin akwatin gawar Sarauniyar a babban zauren taron Westminster.

WASHINGTON, DC - Bidiyon da aka dauka daga sararin samaniya a birnin Landan ya nuna yadda masu alhini suka yi dafifi a bakin rafin Thames da kuma tsallaken gadar Tower Bridge, da ke da tazarar kilomita kimanin 5.6. Jami’ai na sa ran mutune 750,000 za su je yi wa gawar sarauniyar ganin karshe kafin a yi jana’izarta ranar Litinin 19 ga watan Satumba, 2022.

Zauren taron na Westminster zai kasance a bude tsawon sa’o’i 23 a kullum don masu kai ziyara, kuma sojojin masarautar ne za su yi gidan wurin.

Ranar Alhamis fadar Buckingham ta fidda tsarin abubuwan da za a yi a hukumace, har zuwa ranar Litinin da za a yi jana’izar. A ranar Juma’a, Sarki Charles III da ’yan uwansa za su yi taron addu’o’i na dare a wurin akwatin gawar mahaifiyarsu da ke Westminster Hall tsawon minti 15, kamar yadda suka yi a farkon mako a lokacin da aka ajiye akwatin gawar a majami’ar St. Giles Cathedral da ke Edinburgh.

Ana sa ran kimanin baki 2,000, ciki har da shugabannin kasashe da sauran manyan baki za su halarci taron jana’izar a Westminster Abbey. Jim kadan bayan haka, kowa a fadin Biritaniya zai yi shiru tsawon minti biyu, don ba ‘yan kasar damar yi wa sarauniyar karramawar karshe.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG