Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jana'izar Sarauniya Elizabeth: An Sake Dage Wasanni Uku A Gasar Premier


Lokacin da aka dakko akwatin gawar Sarauniyar Ingila, Elizabeth II a ranar, 12 ga watan Satumba 2022.

Daga cikin wasannin da aka dage akwai wanda Manchester United za ta buga a gida tare da Leeds sannan an dage wasan Liverpool da Chelsea wanda za a buga a ranar Lahadi.

Hukumar da ke shirya gasar Premier League ta Ingila, ta sake dage wasanni uku da za a buga a karshen mako mai zuwa.

An dage wasannin ne a wani mataki na nuna girmamawa ga shirye-shiryen jana’izar Sarauniyar Ingila Elizabeth II da za a yi kamar yadda AP ya ruwaito.

An dage wasan Manchester United da za ta buga a gida tare da Leeds sannan an dage wasan Liverpool da Chelsea wanda za a buga a ranar Lahadi.

Baya ga haka, an dage wasan Brighton da Crystal Palace kamar yadda aka tsara a baya. An dage wannan wasa ne sanadiyyar yajin aikin da ma’aikatar fannin sufurin jirgin kasa za su yi.

Yanzu wasannin da za a yi a zagayen gaba sun rage guda bakwai.

A karshen makon da ya gabata, an dage dukkanin wasanni 10 da ya kamata a buga, domin a nuna girmawa ga marigayiyar basarakiyar wacce ta rasu a ranar Alhamis tana da shekaru 96.

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG