Accessibility links

Dubun Masu Fasa Bututun Man Fetur ya Cika a Jihar Filato


Aikin hako man fetur

Satar man fetur ko danye ko wanda aka tace abu ne dake son zama ruwan dare gama gari a Najeriya, to sai dai wasu dubunsu ya cika a jihar Filato

Rundunar tsaro da ake kira Civil Defence dake jihar Filato ta bayyana satar man fetur da fasa bututun mai a matsayin dalilan da suka sa man fetur baya isa wasu jihohin arewa maso gabashin kasar Najeriya.

Shugaban runrunar na jihar Filato Vincent Bature ya yi wannan furucin lokacin da rundunar ta kama wasu barayi da suka fasa bututun man fetur dake wajejen Mista Ali a jihar. Barayin sun fasa bututun man da ya fito daga matatan mai dake Kaduna zuwa Filato daga inda a ke jigilar man zuwa jihohin arewa maso gabas. Shugaban ya ce a cikin'yan kwanakin nan sun samu nasarar cafke barayin man fiye da arba'in da biyar wadanda tuni aka gurfanar da su a gaban kulia.

Vincen Bature ya ce wadanda suka nuna sun kamasu da man fetur ne da kuma gas. Ya ce sun fi satar gas wanda suke zuwa su sayar a kasuwar bayan fagge. Sabili da haka samun mai a garin Bauchi ya yi wuya sai dai a je jigilarshi daga Fatakwal domin barayin sun fasa bututun dake kawo mai daga Kaduna.

Dangane da kokarin da gwamnatin tarayya ke yi domin dakile matsalar Vincent Bature ya ce an ba hukumarsa da sauran hukumomin tsaro aikin tsaron bututun. Ya ce da zara sun kama mutane suna gurfanar da su gaban kotun gwamnatin tarayya ba tare da bata wani lokaci ba. Kawo yanzu akwai wadanda aka hukunta a kurkuku. Wasu an dauresu shekaru 20 ko fiye ma. Akwai wani ma da aka daureshi shekaru 30.

Dangane da masu sayan kayan sata Vincent Bature ya ce daga wadanda suka kama yanzu zasu yi bincike su kaiga kamasu.

XS
SM
MD
LG