Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duk Da Kalubalen Da Muke Fuskanta, Yanzu Mun Shirya Tsaf A Dama Da Mu A Fagen Siyasa - Matan Najeriya


Hotunan Hajiya Aisha Buhari yayin da ta karbi bakuncin mata yan jami'iyar APC a fadar shugaban kasa, Abuja

Duk da yawan mata da kuma yadda suke fitowa kwansu-da-kwarkwatarsu su jeru a kan layi don dangwala kuri’arsu a lokutan zabe, ‘yan tsiraru ne  ke samun mukaman siyasa.

Mata a bangarorin Najeriya daban-daban musamman a arewacin kasar, sun fara fitowa tare da daura damarar ganin an dama da su a fagen siyasar kasar a zaben shekarar 2023 da ma bayan zaben duk da kalubalen kudi, rashin karbuwa daga bangaren abokan tarayyarsu maza da iyalansu, siyasar uban gida, da kuma tsoron rashin samun nasara a zaben fitar da gwani da dai sauran matsaloli da suke fuskanta.

A cikin mata dake fagen siyasar Najeriya musamman a arewa wadanda ke neman a dama da su din, Malma Amina Ibrahim B.B. Faruk, ‘yar takarar majalisar wakilan tarayya ce da ke neman ta wakilci mazabar Gezawa da Gabasawa a jihar Kano wacce ta sami nasara a zaben fitar da gwani karkashin inuwar babbar jam’iyyar adawa ta PDP.

Malama Halima Tahir, mai fafutukar ganin cewa an baiwa mata dama a fannonin rayuwa daban-daban ciki har da siyasa, ta nuna shakku kan a ba wa mace shugabancin kasa a bisa dalilan addini da al’ada, tana mai cewa mata su ne matsalar kansu.

Duk da yawan mata da kuma yadda suke fitowa kwansu-da-kwarkwatarsu su jeru a kan layi don dangwala kuri’arsu a lokutan zabe, a bayan zabe ‘yan tsirari ne ke samun mukaman siyasa in ji ‘yar fafutukar nemawa mata, matasa da kananan yara ‘yancinsu a kasar, Malama Maryam Mamman Nasir.

Da ta ke sharhi kan wannan batu, wata da ta nemi tikitin takarar shugabancin Najeriya karkashin inuwar jam’iyyar SDP a zaben fitar dan takarar shugaban kasa na baya-bayan nan, ta ce lokaci ya yi da za’a jarraba mata saboda a cewarta babu wani abin a zo a gani da mazan suka tabuka tun waccan lokaci.

Idan za’a kwatanta da shekarun baya za’a iya cewa mata a sassan Najeriya sun yunkuro sosai wajen shiga fagen siyasa musamman ma a neman takarar shugabanci kasa inda aka sami Cesnabmihlo Dorothy Nuhu-Akenova karkashin inuwar jam’iyyar SDP, Uju Ken-Ohanenye karkashin inuwar jam’iyyar APC mai mulki sai kuma sanata Aisha Binani da ta sami tikitin gwamna a jihar Adamawa da dai sauransu.

Saurari cikakken rahoton Halima AbdulRa'uf:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:46 0:00

Dubi ra’ayoyi

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG