Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kano Ta Kaddamar Da Shirin Allurar Rigakafin Corona Na Bai-Daya


Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje (Facebook/Gwamnatin Kano)
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje (Facebook/Gwamnatin Kano)

Makonni kalilan bayan bullar sabon nau’in cutar Corona da ake yiwa lakabi da Omicron, gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da shirin allurar rigakafi na bai-daya a fadin jihar, sai dai wasu daga al’ummar jihar na nuna rashin sha’awarsu ga allurar.

A farkon mako ne gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da shirin, inda ya ce yanzu gwamnati za ta maida hankali ga al’umar sassan jihar bayan kammala aikin rigakafin ga kebantattun rukunin mutane da yanayin aikin su ke sanyawa su fuskanci hadarin saurin kamuwa cutar ka COVID-19.

Dr. Tijjani Hussaini shi ne kodinatan kwamitin yaki da Corona a Kano kuma shugaban hukumar lafiya a matakin farko ta jihar, ya kuma fayyace hanyoyin da suka tsara gudanar da riga kafin.

Ya zuwa yanzu dai tuni wasu daga cikin mutanen Kano suka amince tare da karbar wannan riga kafin tun a karon farko saboda gamsuwa da bayanan mahukuntan kasar akan.

Kodayake wani magidanci mai suna Hamisu Yahaya ya lamunce an yi masa allurar, amma yace tilas ce ta sanya ya yarda da ita.

To amma Malam Bashir Muhammad, wani dattijo mai fiye da shekaru 60 yace ba zai amince a yi masa wannan allura ba.

Ga alama dai, akawai jan aiki a gaban hukumomin lafiya na jihar Kano, musamma kwamitin yaki da cutar Corona na jihar da kuma hukumar lafiya a matakin farko a jihar ta Kano.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00


XS
SM
MD
LG