Accessibility links

Duk Dan Arewa Na Zaune Cikin Bakin Cikin Tashin Hankalin Dake Faruwa – In Ji Reverend Musa Asake

  • Garba Suleiman

Babban sakataren na kungiyar Kiristoci ta Najeriya yace wannan tashin hankali dake wakana ya nakkasa tattalin arzikin Arewacin Najeriya da jfa al'ummar yankin cikin kunc in rayuwa.

Babban sakataren kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, Reverend Musa Asake, ya bayyana takaicin yadda tashin hankali a yankin arewacin Najeriya ya nakkasa harkokin kasuwanci da tattalin arziki tare da jefa al'umma cikin fargaba da kuncin rayuwa.

Rev. Asake, wanda yake magana a cikin shirin wanzar da zaman lafiya a arewacin Najeriya na VOA Hausa, yace tun fil azal, Musulmi da Kirista na arewacin Najeriya su na zuwa makaranta tare, aiki tare, zama tare, ko yatsa babu mai nuna ma wani, amma yau an wayi gari sai fitina da rashin jituwa.

Yace zai yi wuya a ce wannan lamari na Boko Haram dake faruwa a Najeriya ba a sunsuno shi tun kafin ya kawo haka ba, saboda haka an yi sakaci wajen daukar matakan da suka kamata na dakile shi tun kafin ya kai inda ya kai.

Yayi kira ga shugabannin arewa da su hada kai, su kira taron koli, da aniya guda ta kawo karshen wannan lamarin, kuma idan har da gaske zasu yi, to za a yi mamaki domin kuwa lamari ne da za a iya magance shi idan an mike an fitar da siyasa daga cikinsa.
XS
SM
MD
LG