Accessibility links

Jami’ai suka ce an gwabza wannan fada ran alhamis, kimanin kilomita 85 a kudu da Maiduguri, inda ‘yan Boko Haram suka fi karfi.

Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram su 9 a lokacin wata musayar wuta a yankin arewa maso gabashin kasar.

Jami’ai suka ce an gwabza wannan fada ran alhamis, kimanin kilomita 85 a kudu da Maiduguri, inda ‘yan Boko Haram suka fi karfi. Alkaluma na nunin cewa dubban mutane suka mutu cikin shekaru hudun da suka shige a dalilin wannan tawaye na kungiyar Boko Haram.

Wani kakakin rundunar sojojin Najeriya, leftana kanar Mohammed Dole, yace soja guda daya ya ji rauni a wannan ba ta kashin. Yace sojojin sun kwace makamai da harsasai masu yawa daga mayakan na Boko Haram.

Babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da abkuwar wannan lamarin.

Kungiyar Boko Haram ta fara tayar da kayar baya tun 2009 a bisa gurin neman kafa dokar Islama a arewacin kasar inda Musulmi suka fi yawa.
XS
SM
MD
LG