Accessibility links

Najeriya Na Neman Taimakon Kamaru Wajen Yakar Boko Haram


Shugaba Paul Biya mai mulkin kasar Kamaru tun shekarar 1982.

Janar J.B. Samuel, shugaban tawagar Najeriya a Kwamitin Tsaron Bakin Iyaka na Najeriya da Kamaru yace ta haka ne kawai zasu iya murkushe Boko Haram

Najeriya ta ce tana bukatar taimako daga kasar Kamaru ta hanyar kara karfin tsaron bakin iyakarta, a yayin da take kokarin murkushe mayakan kungiyar Boko Haram masu kishin Islam.

Matakan sojan da gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta dauka sun sanya mayakan Boko Haram shiga cikin dazuzzuka na can kuryar arewa zuwa bakin iyakar kasar da Jamhuriyar Nijar, da kuma cikin duwatsun dake gabas a bakin iyakar Najeriya da Kamaru.

'Yan bindigar Boko Haram su na amfani da wadannan wurare wajen kai hare-hare. A cikin 'yan kwanakin nan ma, hare-haren da mayakan kungiyar suka kai yayi sanadiyyar mutuwar fararen hula akalla 70 a Jihar Borno na arewa maso gabashin kasar.

Bakin iyakar Najeriya da Kamaru tana da tsawon kilomita dubu daya da dari bakwai, kuma ta taso tun daga tekun Atlantik a kudu har zuwa tabkin Chadi a arewa.

Shugaban tawagar Najeriya a Kwamitin Tsaron Bakin Iyaka na Najeriya da Kamaru, Janar J.B. Samuel, ya fadawa 'yan jarida a wurin wani taron kwamitin cewa, "lallai muna bukatar hadin kai da tallafin Kamaru domin mu murkushe kungiyar Boko Haram mai kishin Islama."

Wani jami'in yankin arewacin Kamaru yace kasarsa ta riga ta dauki matakan da suka dace na karfafa tsaro a bakin iyakarta da Najeriya, amma bai yi karin haske kan matakan ba.
XS
SM
MD
LG