Accessibility links

Kungiyar ECOWAS zata shiga tsakani a kasar Guinea-Bissau


Wani soja yana sintiri a Bissau

Kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS, zata tura wata tawagar sojoji zuwa kasar Guinea- Bissau

Kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS, zata tura wata tawagar sojoji zuwa kasar Guinea- Bissau yau Litinin, a yunkurinta na shawo kan rudanin siyasa a kasar.

Al’ummar kasa da kasa, da kasashen nahiyar Afrika da kuma sauran kasashen duniya sun kushe da kakkausar murya, juyin mulkin da aka yi a kasar makon jiya, suka kuma yi kira da a koma mulkin farin hula.

A cikin sanarwar da kungiyar ta bayar jiya Lahadi, babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya jadada cewa, yana sa ido sosai kan lamarin, yana kuma matsa lamba domin ganin an sami zaman lafiya da oda a harkokin siyasar kasar.

Jam’iyun siyasar kasar Guine-Bissau sun shafe kwanaki suna tattaunawa da shugabannin juyin mulkin. Kakakin jam’iyun, Femando Vaz ya bayyana cewa, za a cimma matsaya yau Litinin.

Kwace mulkin da aka yi ranar Alhamis ya gurguntar da kamfen zaben shugaban kasa zagaye na biyu da ake shirin gudanarwa a kasar dake yammacin Afrika, ranar 29 ga wannan watan na Afrilu.

Tsohon Firai Minista Carlos Gomes, wanda shi dan jam’iya mai mulki ne, ya ba abokin hamayyarshi Kumba Yala tsohon shugaban kasar, wanda kuma yake da dangantaka ta kut da kut da rundunar sojoji, kyayyawar rata.

Sojojin juyin mulkin sun kama Mr. Gomes da shugaba mai ci yanzu, Raimundo Pereira a gidajensu. Ya zuwa jiya Lahadi, ba a san inda suke ba.

XS
SM
MD
LG