Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EFCC Zata Nemi Ma’aikatan Banki Su Bayyana Kaddarorin Su


Abdulrasheed Bawa.
Abdulrasheed Bawa.

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzkikin kasa zagon kasa a Najeriya ta bayyana cewa, daga ranar 1 ga watan Yunin shekarar 2021, za ta fara neman ma’ikatan banki a fadin kasar su nuna bayanan kaddarorin da suka mallaka.

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzkikin kasa zagon kasa a Najeriya ta bayyana cewa, daga ranar 1 ga watan Yunin shekarar 2021, za ta fara neman ma’ikatan banki a fadin kasar su nuna bayanan kaddarorin da suka mallaka domin taimaka wa aikin yaki da masu yi wa tattalin arzkikin kasa ta’anati.

Shugaban hukumar EFCC, Abdurashid Bawa ne ya bayyana hakan biyo bayan ganawa da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a Fadar Aso rock da ke birnin tarayyar kasar.

A cikin sanarwar da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa, daga ranar 1 ga watan Yuni, za ta tabbatar da cewa ma’aikatan banki suna cika takardun bayanan kadarorin da suka mallaka tare da yin bita a kan bin umarnin da kuma aiwatar da umarnin.

Karin bayani akan: EFCC​, Abdurashid Bawa​, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Hukumar EFCC dai ta ce, ta dauki wannan matakin ne sakamakon damuwa da masu ruwa da tsaki su ka nuna a kan gagarumin gudunmuwar da ma’aikatan banki ke bayarwa a yaki da matsalolin da suka shafi cin hanci da rashawa a kasar duba da yadda masu aikata laifuffukan ruf da ciki da kudadden al’umma ke neman su yi amfani da kudadden sata a koda yaushe ta bankuna.

Shugaban EFCC dai, ya kara jadada cewa, za a bukaci ma’akatan bankuna su na bayyana kaddarorin da suka mallaka kuma hukumar za ta tabbatar da cewa, dukannin ma’aikatan bankuna a Najeriya sun bi wannan doka, ya na mai kara tabbatar wa ‘yan kasar cewa, daga yanzu, hukumar EFCC zata yi duk mai yiyuwa wajen tabbatar da cewa, ta kawo karshen laifuffuka da suka shafi almundahana a kasar.

Sabon Shugaban Hukumar EFCC Ta Najeriya Bai Ba Da Kunya Ba

Sabon Shugaban Hukumar EFCC Ta Najeriya Bai Ba Da Kunya Ba
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

XS
SM
MD
LG