Accessibility links

Ekiti: Shugabannin Addinai Sun Yi Kiran Zaman Lafiya


Taron shugabannin addinai kan zaman lafiya a jihar Plateau, Nigeria

An yi kiran zaman lafiya a jahar Ekiti da ke kudu maso yammcin Najeriya bayan da rikicin kabilanci ya barke a jihar a makon da ya gabata.

Shugabannin addinai a jahar Ekiti da ke Kudu maso yammcin Najeriya, sun yi kira da a zauna lafiya bayan wani rikici mai kama da na kabilanci ya barke a jahar a makon da ya gabata.

“Ya kamata a daina kawo fitina da tashin hankali da tarwatsa jama’a ko kai musulmi ne ko kirista, ya kamata a rungumi juna a zauna lafiya.” Inji Sheikh Abdurrahman Olurekemi.

Ana shi bangaren, Pastor Kola Ajayi ya bukaci jama’a da su hada kai sannan su zauna lafiya da juna domin samun ci gaba.

Wani mazaunin garin Ado Ekiti da ya zanta da wakilin Muryar Amurka, ya ce mutanen arewa da dama sun fice daga cikin birnin.

“Hausawan da ke cikin gari idan aka kasa su kashi kashi goma, kashi takwas sun tafi gida.” Inji mazaunin garin Ado Ekiti a tattaunawarsu da wakilin Muryar Amurka.

Rikicin a cewar wannan mazaunin garin da ya nemi kada a ambaci sunansa, ya samo asali ne bayan da wasu ‘yan damfara suka cuci wata mata, wacce ta je ta kira mijinta domin a kwatar mata hakkinta, lamarin da ya sa ‘yan damfarar suka rufe mijin da duka.

Ya kara da cewa Yarbawa sun zargi ‘yan arewa da cewa su suka san ‘yan damfarar duk da cewa wadanda suka yi damfarar ma Yarbawa ne.

Yanzu haka babu wani labari da ke nuna cewa an rasa rayuka, yayin da aka kafa dokar hana fita a garin na Ado Ekiti.

XS
SM
MD
LG