Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

El Rufai Ya Saka Tukwici "Mai Tsoka" Ga Duk Wanda Ya Fadi Inda Shugaban NLC Ayuba Wabba Yake


Gwamna Malam Nasiru El Rufai (Twitter/ Kaduna Government)
Gwamna Malam Nasiru El Rufai (Twitter/ Kaduna Government)

“Ana neman Ayuba Wabba da wasu shugabannin kungiyar kwadago ta kasa saboda zagon kasa da suke yi wa tattalin arzikin jihar da kuma kassara ayyukan wasu ababen more rayuwa.”

Hukumomi a jihar Kaduna​ da ke arewa maso yammacin Najeriya, na neman shugabannin kungiyar kwadago ta kasa ruwa a jallo saboda abin da ta kira zagon kasa da suke yi wa jihar.

Gwamna Malam Nasiru El Rufai ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter a ranar Talata, inda ya ce akwai tukwici da za a ba duk wanda ya bayyana inda Waba yake.

“Ana neman Ayuba Wabba da wasu shugabannin kungiyar kwadago ta kasa saboda zagon kasa da suke yi wa tattalin arzikin jihar da kuma kassara ayyukan wasu ababen more rayuwa.”

Gwamnan ya kara da cewa, “duk wanda ya san inda ya buya ya aika sako zuwa ga ma’aikatar shari’a ta jihar Kaduna @MOJKaduna KDSG, akwai tukwici mai tsoka da za ba shi.”

Karin bayani akan: El Rufai, NLC, jihar Kaduna​, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Ana ta kai ruwa tsakanin kungiyar kwadago ta jihar Kaduna wadanda suka samu goyon bayan reshensu na kas akan korar wasu ma’aikata da gwamnatin jihar ta yi.

A ranar Litinin Wabba ya jagoranci wata zanga-zanga ma’aikata a jihar ta Kaduna don yi wa gwamnati gargadi kan korar sama da ma’aikatan dubu bakwai da ta yi a matakan kananan hukumomi da na jiha.

Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC, Ayuba Wabba yana jawabi a wajen zanga-zangar (Twitter/NLC)
Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC, Ayuba Wabba yana jawabi a wajen zanga-zangar (Twitter/NLC)

Sai dai Wabba ya kara nanata cewa, kungiyar ta NLC ba za ta janye zangar-zangar da take yi ba.

“Shugabanninmu suna nan kwansu a kwarkwatarsu, muna tare da ku a kowane a hali, ya zama dole mu kare hakkin kowane dan Najeriya.” Wabba ya ce, a wani bidiyo da NLC ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Litinin.

Zanga-zangar ta kai ga aka dauke wutar lantarkia daukaicn jihar, tare da rufe tashar saukar jiragen sama.

Har ila yau, zanga-zangar ta haifar da dogayen layukan shan mai a sassan jihar.

Gwamnatin jihar ta Kaduna​ ta yi Allah wadai da wannan zanga-zanga inda ta zargi kungiyar ta kwadago da shugabannin da yunkurin kassara tattalin arzikin jihar.

XS
SM
MD
LG