Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ellen Johnson Sirleaf Ta Zama Shugabar ECOWAS


Shugabar Liberia Ellen Johnson Sirleaf ta dare karagar shugabancin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta ECOWAS, tare da yin alkawarin ganin samun nasarar yunkurin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Inda ta kara da yin kira ga sauran kasashen da suke membobin kungiyar da su kara zage damtse wajen ganin an murkushe ta’addanci. Shugaba Sirleaf ta maye gurbin Shugaba Macky Sall na Senegal da ya jagoranci kungiyar.

An gabatar da zabenta ne a babban taron shekara-shekara na ECOWAS da aka yi a cikin karshen makon da ya gabata a birnin Dakar din ta Senegal. Wata sanarwar da ta fito daga ofishin Shugabar, ta bayyana kiran karkare magana.

Game da maganar daukar mataki a dokance don rayawa da kuma kawo gamayyar kasuwanci tsakanin kasashen Afirka ta Yamma. Sirleaf ta kuma yi alkawarin inganta daidaiton hada-hadar kudi.

Inda wani daraktan cibiyar bincike ta kasashen Afrika ta Yamma Ousman Sene ya bayyana cewa, daidaiton hada-hadar kudi ta kasashen, musamman wajen yi kudin da zasu yi amfani bai daya, to zai inganta wannan kuduri na tattalin arzikin nahiya.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG