Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ethiopia Ta Zargi Masar Da Zuga 'Yan Tawayen Kasarta


Gwamnatin Ethiopia tana zargin Masar da iza yan tawayen kasar, wanda hakan ya tilastawa Ethiopian ta kafa dokar ta baci a shekaranjiya Lahadi.

Ethiopia tace tana da shaida mai yawa dake tabbatar da ana horar da yan tawayen, ana basu tallafin kudi a Masar, inji kakakin gwamnatin Ethiopia, Getachew Reda a hirarsa da manema labara a jiya Litinin.

Tun cikin makon jiya dai kasar Masar take ta musunta bada wani taimako ga ‘yan tawayen na Ethiopia.

Masar da Ethiopia sun dade suna samun rikici tsakaninsu a kan atun mallakar ruwan kogin Nilu, inda Masar ke cewa madatsar ruwan da Ethiopia ke ginawa a kogin zai rage yawan ruwan da Misra din ke samu.

Getachew yace dokar ta bacin watanni shidan da aka kafa zata baiwa gwamnati daman daukan kwararan matakai a kan kungiyar OLF da ta shirya tarukan zanga zanga a duk fadin jihar Oromia a makon da ya gabata.

Kungiyoyin kare hakkin Bil Adama da jami’an ‘yan adawa sunce mutane akalla 400 ne aka kashe a wannan zanga zanga ta kin jinin gwmanti a shekara da ta gabata.

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG