Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Takarar Shugabancin Amurka Sun Tafka Muhawara A Karo Na Biyu


Jiya ‘yan takaran shugaban kasa a zaben wannan shekara a Amurka, Hillary Clinton da Donald Trump sun yi muhawarsu ta biyu inda suka gwabza akan batutuwa da dama da suka shafi halin zaman rayuwar, shirin kiyon lafiya na shugaba Obama da kuma matsayin danatakar Amurka da kasashen ketare.

Daya daga cikin abubuwan da aka tambaye su shine matsayin Musulmin dake zaune a Amurka, wadanda a can baya, Donald Trump yace zai hanawa shigowa kasar in yaci zabe.

Donald Trump yace: Ko ana so, ko ba’a so, kuma duk yadda muke son mu gyara maganar saboda siyasa, tilas a dauka cewa akwai matsala. Dole ne Musulmi su rinka bada bayanai idan sun ga ana wani abinda ba daidai ba, ko suka ga wasu na wani abinda ke nuna kiyayyar wani jinsi, alal misali kamar abinda ya faru a birnin San Bernandino, mutane da yawa sun ga bama-bamman mutanen nan nan biyu da suka kai hari a garin, suka hallaka mutane 14, suka raunana wasu da yawa.”

A nata bangaren, Hillary Clinton tace tana son a darajanta kowa a Amurka, ba tareda la’akari da addininsa ko jinsa ba, duk da cewa tana sane da matsalolin da Musulmi suka jima suna fuskanta a Amerika.

Hilary Clinton tace: “Abin bakin ciki ne ganin cewa an dade ana fadar abubuwan da basu dace ba akan Musulmi. Ni ina son in jagoranci Amurka inda kowa yake da daraja da kima, wurin da, muddin zaka zage dantse kayi aiki tukuru, ka taimakawa al’ummar da kake zaune a cikinsu, to haka Amurka take kuma haka ya kamata ta ci gaba da kasancewa don anfanin ‘ya’yanmu da jikokinmu.”

XS
SM
MD
LG